<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Kowace Rana Akwai Jaraba LW447</title>
<lyrics>[V1]
 1) Kowace rana akwai jaraba
 zuwa ga dukan masu binsa
 Duk da hakanan muna aniya,
 ba za mu ba Shaiɗan dama ba.

[V2]
 KORUS
 An jima za mu riƙa nasara.
 Babu jaraba da za ta zo.
 Mu tada muryar, mu yi waƙarmu.
 Ba za mu ba Shaiɗan dama ba.

[V3]
 2) Lokacin da mutuwa ta sabko
 ta ɗauki ƴaƴan tumakinmu,
 Kada wannan ya sa mu ji tsoro.
 Ba za mu ba Shaiɗan dama ba.
 Korus

[V4]
 3) Bari mu mutu cikin hannunsa,
 mu riƙe bangaskiyarsa sosai,
 domin mu gaji mulki na sama
 wanda Yesu yake shiryawa.
 Korus

[V5]
 4) Mu tuna da ranar zuwan Yesu.
 Duk masu bi za su yi murna,
 kowace gwiwa za ta rusuna,
 marasa bi za su yi kuka.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>447</hymn_number>
</song>